'Yan adawa sun kabsa da 'yansanda a Iran

Zanga-zanga a birnin Tehran Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ko wane irin goyon baya 'yan adawar ke da shi?

Mummunan fada ya barke tsakanin masu zanga-zanga da 'yan sanda a Tehran, babban birnin Iran, yayin da masu adawa da gwamnati ke cigaba da zanga-zanga a sassa daban-daban na birnin.

Dubban mutane ne dai suka shiga zanga-zangar da 'yan adawa suka kira domin nuna goyon baya ga boren da aka yi a Tunisia da kuma Masar.

Wakilin BBC ya ce, “Wannan dai shi ne bore ga gwamnatin Iran mafi girma cikin shekara guda.

Hakan kuma yana nuna cewa, 'yan adawa dake da alamar launin kore suna nan a kan bakansu na kalubalantar gwamnati..

Ya zuwa yanzu dai an kama 'yan