An kashe masu gadi biyu a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan dai shi ne harin bam karo na biyu cikin kusan makonni biyu a birnin

Wasu masu gadi biyu sun mutu yayin da wani dan kunar bakin wake yayi kokarin kutsawa cikin wani rukunin shaguna a Kabul, babban birnin Afghanistan.

Budewa dan kunar bakin waken wuta da jami'an tsaro suka yi ne ya haddasa tashin bam din da ya kuma hallaka dan kunar bakin waken:

Wannan dai shi ne harin bam karo na biyu cikin kusan makonni biyu a birnin na Kabul, a cewar Wakilin BBC a Afghanistan.

Tuni dai 'yan sanda suka killace yankin da lamarin ya auku.

Koda a watan da ya gabata dai mutane tara ne suka hallaka sakamakon wani harin da dan kunar bakin wake ya kai a wani babban shago.