Farashin kayan abinci na tashin gwauron zabi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Farashin ya karu da kashi 15% daga watan Oktoban da ya gabata zuwa Janairun bana

Wata kididdiga da babban bankin duniya ya fitar, ta nuna cewa karuwar farashin kayan abinci ta jefa mutane miliyan 44 cikin talauci daga watan Yunin da ya wuce.

Kamar yadda kididdigar bakin ta baya-bayan nan ta nuna, farashin ya karu da kashi 15% cikin dari daga watan Oktoban da ya gabata zuwa Janairun bana.

Hauhawar farashin dai ta fi shafar talaka wanda ke kashe fiye da rabin abin da yake samu a kan abinci.

Bankin ya yi kira ga taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 da ya yi kokarin shawo kan lamarin.

Shugaban bankin duniya Robert Zoellick, ya fada a wata sanarwa cewa: "Farashin kayan abinci a duniya na tashi zuwa wani yanayi mai hadari, inda yake baraza ga miliyoyin mutane."

Ya kuma ce tashin farashin na da alaka da boren da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya, duk da cewa ba shi ne musabbabi ba.

A wani rahoton na daban da ta fitar a farkon watan nan, Hukumar Kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO), ta ce farashin kayan abinci ya kai makura a watan Janairu. Nan gaba a makon nan ne ministocin kudi na kasashe masu tasowa da wadanda suka ci gaba za su yi taro a birnin Paris na kasar Faransa.