An yi kira da a kashe 'yan adawar Iran

Masu zanga-zanga a Iran Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga-zangar adawa da gwamantin Iran suna fito-na-fito da 'yan sanda

'Yan majalissar dokokin kasar Iran fiye da 200 ne suka nemi da a yanke hukuncin kisa kan wasu fitattun 'yan adawa biyu na kasar.

An nemi a tuhumi Mr Hossein Mousavi, da kuma Mehdi Karroubi, a gaban kuliya bisa laifin cin amanar kasa.

Gidan talbijin na kasar ya nuna wasu 'yan majalisar dokokin a fusace a zauren Majalisar suna yin Allah wadai da abun da suka kira gangamin da ya sabawa shari'a.

Sannan suka yi kiran da a aiwatar da hukuncin kisa a kan Mr Mousavi da kuma Mr Karroubi.

A jiya Litinin a ka yi a rangama a tsakiyar birnin Tehran a lokacin da 'yan sanda suka yi amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga-zangar nuna kyamar gwamnati.

Karin bayani