Yan gudun hijira a kasar Italiya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan gudun hijira daga kasar Tunisia

Hukumomin garin tsibirin Lampedusa a Italiya sun ayyana dokar ta baci, sakamakon yadda 'yan gudun hijira daga kasar Tunisia suke ta shigowa tsibirin.

A makon daya gabata kadai, fiye da 'yan gudun hijira dubu hudu ne suka iso zuwa tsibirin ta jirgin ruwa .

An tafi da kusan rabin 'yan gudun hijrar zuwa Siciliy amma ana tsammanin wasu 'yan gudun hijirar zasu dada tsallakowa a 'yan kwanaki masu zuwa.

Ministan cikin gidan Italiya Roberto Malini ya ce yana da mahimmanci hukumar tarayyar turai da shugabannin kasashen turai, su fara daukar wani kwarkwaran matakin diplomaciya ga dukkanin kasashen da wannan lamari na 'yan gudun hijira zai shafa.