Yau ake bukin Mau'ludi

Image caption Wani masalaci a birnin Landan

A yau ne ake gudanar da bukukuwan mauludi a Najeriya da wasu kasashen musulmi na duniya ,domin tunawa da ranar da aka haifi manzon Allah SAW.

Yau din dai rana ce ta hutu a Najeriyar, rana ce kuma da musulmi ke gudanar da adduo'i da kuma bukukuwa domin muhimmancin ta.

To amma sai dai yayin da wasu ke ganin wannan rana ce ta musamman, suke kuma bukukuwan zagayowar ta, wasu tsakankanin musulmi na ganin kowacce rana ma, rana ce daya kamata a rika tunawa da Manzon Allah SAW, a saboda haka suke ganin babu dalilin yin bikin mauludin.