'Yan Najeriya sun bude asibitocin karya a Afrika ta Kudu

Afrika ta Kudu
Image caption Hukumomi na tsoron mutanen sun yiwa dubban marasa lafiya magani ba bisa ka'ida ba

Za a gurfanar da wasu 'yan wasan Najeriya a gaban kotu a Afrika ta Kudu, bisa zargin aiki a matsayin likitocin boge da kuma bude asibitoci.

An kuma tuhumi mutanen da laifin jefa rayuwar jama'a cikin hadari.

Ana zargin mutanen da gudanar da asibitoci shida a wasu gundumomi uku na kasar.

Hukumar bincike mai zaman kanta a Afrika (CIS), ta ce fannin lafiya na daga cikin fannonin da aka fi yin damfara a cikinsu a Afrika ta Kudu.

Kamar yadda bincikenta ya nuna, masu aiki da takardun karya sun kai kashi 15% cikin dari ko kuma 18% cikin dari a duka fadin kasar.

Ana saran 'yan Najeriyar biyar za su gurfana a gaban kuliya a gundumar Mpumalanga, tare da wasu likitocin kwarai biyu daga Najeriyar, wadanda suka amince aka yi amfani da takardunsu wajen yiwa na bogen rijista.

Hukumar kula da lafiya ta kasar ta ce tana tsoron mutanen sun yiwa dubban marasa lafiya magani ba bisa ka'ida ba.

Mahukunta na kuma binciken rahotannin da ke cewa akwai wasu mutane 17 da ke duba jama'a a asibitocin gwamnati da masu zaman kansu.

A makon da ya gabata, an kama wani mutum da ya yi da'awar likita ne bayan matar da ya yiwa tiyata ta rasu a Gabashin gundumar Cape.