Shugaba Obama ya soki Gwamnatin Iran kan masu zanga zanga

Shugaba Obama ya yi mummunar suka a kan kasar Iran, yana mai cewar a yayin da mahukuntan kasar ta Iran suke murna tare da buki a kan faduwar gwamnatin kasar Masar, amma sun lakadawa 'yan kasarsu da suka yi zanga zangar lumana dukan tsiya.

Shugaba Obama ya ce Amurka ba zata ce ga abun da ya kamata mutanen Iran su yi ba, to amma yana fatan masu zanga zangar zasu samu karfin guiwar ci gaba da zanga zangarsu.

Yace "abun da ya kamata ya zama daidai a Masar, to ya kamata ya zama daidai a Iran, wannan kuwa shi ne kamata yayi ace mutane suna da 'yancin bayyana ra'ayinsu da korafinsu, sannan kuma su bukaci samun gwamnati da za ta tausaya musu".

Shugaba Obama ya ce matakan farkon da mahukuntan sojin kasar Masar suka dauka suna da karfafa guiwa.