Tallafi ga masu hamayyar siyasa ta intanet

Adawar siyasa ta Intanet Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Akwai masu fafutuka da dama da ke gudanar da ayyukansu ta intanet

Amurka za ta samar da dola miliyan 25 a bana domin taimakawa masu hamayya ta siyasa kaucewa takurawar da suke fuskanta wajen gudanar da ayyukansu ta hanyar sadarwa ta Internet a kasashen da ake mulkin kama karya.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hilary Clinton, ta ce za'a samar da fasaha da kayan aiki, tare da bayar da horo ga masu irin wannan fatutuka ta hanyar internet, domin su yi zarra a kan masu kawo musu cikas.

Ta ce: "Kudurinmu na tabbatar da 'yancin amfani da hanyar sadarwa ta Internet, kuduri ne na tabbatar da 'yan cin jama'a, kuma yanzu muna daukar mataki domin tabbatar da haka.

A cikin 'yan makwannin da suka gabata dai, an yi ta amfai da hanyoyin sadarwa na Internet da kuma wayoyin salula wajen shirya zanga-zanga a kasashe da dama na yankin gabas ta tsakiya.

Kuma hakan ya tilastawa shugabannin kasashen Tunisia da Masar sauka daga kan karagar mulki.