An ga dogayen layuka a bankuna a Cote d Ivoire

Hakkin mallakar hoto AFP

An ga dogayen layuka a bankuna a Cote d Ivoire, bisa tsoron da masu ajiyar kudi ke ji na rushewar bankuna a lokacin da ake cigaba da kalubalantar juna a kan zaben shugaban kasar da aka yi a kasar a baya.

Bankin Starndard Chartered shi ne na hudu da a wannnan makon ya bayyana dakatar da ayyukansa a kasar.

An rufe galibin na'urorin dibar kudi da ke birnin Abidjan, ba a kuma iya karbar kudin duk wani ceki da aka rubuta.

Bankin BCEAO na yankin, a makon jiya ne ya gargadi bankunan kasuwanci cewa za su iya fuskantar takunkumi idan suka ci gaba da harka da gwamnatin Laurent Gbagbo.

Mr Gbagbo ya yi kememe ya ki sauka daga mulki, duk kuwa da amincewa da galibin kasashen duniya suka yi da Alassane Ouattara, a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi a watan Nuwamba a kasar.