Harkokin kasuwanci sun tsaya cik a Jos sakamakon ziyarar Shugaba Goodluck

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Rahotanni daga Jos babban birnin jihar Pilato na cewa, harkokin kasuwanci na fuskantar cikas, sakamakon rurrufe wasu wuraren kasuwancin da jami'an tsaro suka yi, yayin da shugaba Goodluck Jonathan ke ziyartar jihar a yau, a cigaba da yakin neman zabensa.

'Yan-kasuwa na cewa an takura masu.

To amma a cewar hukumomin tsaro, 'yan kasuwar dake zaune a gefen tituna ba bisa ka'ida ba ne kawai aka tasa.

Dama dai ana gudanar da harkokin kasuwanci rabi da rabi ne a birnin na Jos, sabo da yawan tashin hankalin da ake fuskanta a birnin.

Rikice-rikice a wasu jihohin Najeriyar, musamman jahar ta Pilato ba su kamar sa kare, duk kuwa da alwashin da gwamnatin Tarayya ke sha, na shawo kansu.

Bayan rahotannin da gwamnatin ta samu daga kwamitoci daban-daban da ta kafa a baya, majalisar tsaron kasar ta yi tarurruka masu yawa da nufin shawo kan matsalar, amma har yanzu ba ta sake zani ba. Ko a jiya ma an sami hasarar rayuka a jahar Pilato a tashe-tashen hankula.