Mutum daya ya halaka a birnin Jos

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu mazauna birnin Jos

Hukumomin birnin Jos a jihar Plato dake Arewacin Najeriya sun ce an sami wata hatsaniya a jiya , kuma wani dansanda ya mutu.

Kwamishinan 'yansandan jihar Abdulrahaman Akano ya shaida wa manema labarai cewa wasu mutane ne daya kira zauna gari banza suka daba wa dansandan makami wanda ya yi sanadiyyar mutuwar tasa.

Mr Akano ya kara da cewa sun kama wasu mutane da suke zargi da hannu a kisan dan sandan.

Wannan lamari dai ya haifar da rudani a cikin birnin na Jos inda jama'a suka yi ta guje-guje inda wasu rahotanni ke cewa an sami Karin hasarar rayuka a wasu yankuna na birnin a sanadiyar haka, amma dai rundunar 'yansandsan jihar ta ce mutuwar dandan guda kawai ta sani.

Jihar Plato dai na fama da tashe tashen hankula da suka ki ci suka ki cinyewa.