Barkewar tarzoma a kasar Libya

Image caption Shugaba Gaddafi

Rahotannin da ba'a tabatar dasu ba sunce an gudanar da mummunar zanga zanga a birnin Benghazi na kasar Libya.

Wadanda suka shaida lamarin da idanunsu sun shaidawa BBC cewar zanga zangar dai ta biyo bayan kama wani lauya mai sukar gwamantin kasar.

Kodayake ance daga bisani an sake shi amma jama'a basu daina zanga zangar ba.

Wakiliyar BBC ta ce wani wanda ya shaida yadda lamarin ya auku, ya ce cinciridon mutanen sun yi ta rera wakokin nuna kyamar gwamnati, wasu kuma sun yi wa yansanda ruwan duwatsu, inda su kuma yansanda suka maida martani ta hanyar fesawa masu zangar ruwa da kuma harsashen roba da kuma hayaki me sa hawaye.

kimanin mutane dubu biyu ne dai suka gudanar da zanga zangar a cewar wadanda suka ganewa idanunnasu.

Sun kuma ce masu zangar zangar sun yi taho mu gama da magoya bayan gwamantin kasar.