An kashe wani ma'aikacin gwamnatin Amurka

Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Wurin da lamarin ya auku a Mexico

An kashe wani ma'aikacin gwamnatin Amurka a Mexico, yayinda wani ya samu raunuka, bayan da aka kai musu hari a wani babban titi a tsakiyyar birnin Mexico.

Jami'an wadanda ke aiki da hukumar shiga da fice da kuma kwastom , na tuki ne a birnin Mexico zuwa birnin Monterrey dake Arewacin kasar a lokacin da aka kai masu hari .

Jami'an wadanda ba'a bayana sunnyensu ba na aiki ne a hukumar shiga da fice da kuma kwaston a offishin jakadancin Amurka da ke Mexico.

Sai dai ba'a san dalilin da ya sa aka kai masu harin ba, amma daya daga cikin su ya samu munanan raunuka, abun da kuma ya yi sanadiyyar mutuwarsa, yayinda dayan an harbe shi a kafadar sa da kuma kafarsa.

A wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Mexico ta fitar ta yi Allah wadai da harin kuma ta yi alkawarin gudanar da bincike domin gurfanar da wadanda suka aikata wanan aika aikar a gaban kuliya .