Jam'iyyar PNDS na kara samun goyon baya a Nijer

A jamhuriyar Nijar yayin da ya rage kasa da wata gudana a je zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, jam'iyyar PNDS-Tarayya, wadda ta zo ta daya a zagayen farko, tana cigaba da samun goyon bayan wasu jam'iyyu.

Wani bangare na jam'iyyar CDS-Rahama ta tsohon shugaban kasar, ya ce zai marawa dan takarar PNDS-Tarayya, Alhaji Mahamadou Issoufou, a zaben na ranar sha biyu ga watan Maris.

A cewar wannan bangaren a karkashin jagorancin mataimakin shugaban CDS-Rahaman, Alhaji Abdou Labo, shugaban jam'iyyar ne, Alhaji Mahamane Ousmane, ke da alhakin koma bayan da suka fuskanta a zaben kananan hukumomi da na majalisar dokokin da aka gudanar.

Sai dai bangaren Alhaji Mahamane Ousmane din ya ce har yanzu yana kan bakansa na goyon bayan dan takarar MNSD-Nasara, Alhaji Seini Oumarou, a zagaye na biyu.