Amruka: Fashi a tekun Somaliya ya zama kwakkwarar sana'a

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Amruka ta bayyana cewa, lamarin fashi a yankin ruwan Somaliya ya zama wata kwakwarar sana'a fiye da yadda aka zata tun farko, kuma zai fi sauki a kawo zaman lafiya a Afghanistan da a ce za a kawar da fashi a tekun.

Babbar jami'a mai kula da yaki da fashi a tekun, Donna Hopkins, ta gayawa BBC cewa, kadan ne kawai daga cikin dala miliyan sittin din da aka biya a bara, a matsayin diyya, ya shiga hannun 'yan fashin kansu.

Yawancin kudaden sun fada hannun kungiyoyi masu aikata miyagun laifufuka na kasashe, wadanda ke samarwa 'yan fashin bayanai akan jiragen ruwan da suka fi tsoka.