Sabbin bayanai kan shugaban gwamnatin soja na Masar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption wasu masu zanga zanga a Masar

Shekaru Uku da suka gabata wasu ma'aikatan diplomaciyar Amurka, sun bayyana Shugaban rundunar sojin kasar Masar a matasyin wani mutum da baya kaunar a sami sauyi.

Bayanan da shafin wikileaks ya samu wanda kuma aka wallafa a jaridar Daily Telegraph a Birtaniya sun ce Field Marshal Mohammed Dandawi yayi ta amfani da matsayinsa a cikin majalisar ministocin kasar wajen yin adawa da sauye sauye irin na siyasa da kuma tattalin arziki.

Mr Dandawi ya zama shugaban majalisar gwamatin mulkin sojin kasar Masar ne bayan da shugaba Mubarak ya sauka daga kan mulki.

Gwamnatin wucin gadi ta kasar ta dau alkawarin gudanar da sauye sauye irin na siyasa da kuma zabuka a cikin wannan shekarar.