An kaiwa masu zanga zanga hari a Bahrain

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wadanda suka sami raunuka a Baharain

Jami'an tsaro a Bahrain sun kai hari kan wani sansani da masu zanga zangar nuna kin jinin gwamnatin kasar suka kafa, a wani dandali da ke babban birnin kasar na Manama.

'Yan adawa sunce an kashe akalla mutane biyu, an kuma jikkata wasu.

Wadanda suka shaida lamarin sunce 'yan sanda ne suka iso dandalin, su kai ta harbawa masu masu zanga zangar hayaki mai sa hawaye, a lokacin da suke kwance suna bacci.

An dai kori masu zangar zangar daga sansanin ,an kuma bata masu tantunan da suka kafa da kuma kwalayen su.

Masu zanga zangar dai na bukatar ganin cewa an gudanar da sauye sauye a tsarin mulki demokradiyya na Bahrain ,a kasar da yan shi'a ne suka fi rinjaye wadda kuma ke karkashin mulki yan sunni masu sarauta.