Kasafin kudin Najeriya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

Majalisar dattawan Najeriya ta ce a wata me zuwa ne za ta zartar da kasafin kudin kasar na bana.

Ta ce kafin ta je yakin neman zabe, tana kyautata zaton za ta zartar da kasafin kudin .

Senata Nuhu Aliyu dan majalisar dattawan Najeriya ya shaidawa BBC cewa yanzu haka su na kan sauraron bahasin jama'a kan kasafin kudin.

Ya ce akwai wasu ayyukan da suka yi da ya shafi kasafin kudin da ya sa aka samu jinkiri wurin zartarwa.

Wasu masana dai sun ce cigaban kowace kasa ya ta'allaka ga irin kasafin kudin da gwamnati ke warewa domin inganta rayuwar al'umma, sai dai wanan batu na cigaba da kawo koma baya a kasar, saboda matsalar da ake fuskanta wurin aiwatar da kasafin kudin a kowace shekara.