Yakin neman zabe: Jonathan yayi gum kan rikicin Jos

Hakkin mallakar hoto Reuters

Ziyarar da shugaban Nijeriya, Dakta Goodluck Jonathan, ya kai jihar Filato mai yawan fama da rigingimu masu nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa, ta haifar da kace-nace.

Abin da ya janyo kace-nacen dai shi ne yadda shugaban bai ce kala ba kan lamarin jihar duk da tsammanin da jama'ar jihar suka yi, na ji daga bakin shugaban, kan abinda gwamnatin kasar ke yi domin magance matsalar ta jihar Filato.

Dubban mutane ne dai aka kashe a ciki da kewayen Jos babban birnin jihar ta Filato, a 'yan-shekarun nan, kuma yayin da Nijeriyar ke tunkarar zabuka, ga alama lamarin na jihar Filato ya ki ci ya ki cinyewa.