Samar da makamashi a jamhuriyar Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani dan kasar Nijar

Hukumomin jamhuriyar Nijar sun bude wani taro kan yadda za'a samar da makamashi a kasar.

Firaministan kasar, Dakta Mahamadou Danda ya ce gwamnatin kasar na kokarin ganin cewa ta samar da makashi saboda ita ce babbar hanyar da zata bunkasa tattalin arzikin kasar.

Ya kuma ce gwamnati ta na nazari kan kafuwar wata sabuwar tashar samar da makamashi na nukiliya a kasar.

Niger dai na dab da shiga cikin sahun kasashe masu arzikin mai. Sai dai kawo yanzu kasa da kashi daya na 'yan kasar ne, mazauna karkara ke cin moriyar Lantarki, yayinda kasa da Kashi 10 cikin 100 ne ke samun zarafin aiki da makamashi.