An kai hari kan caji ofis a jihar Bauchi

Caji ofis
Image caption Caji ofis

Hukumomin tsaro a Jihar Bauchi a arewacin Nijeriya sun tabbatar da mutuwar mutane 4 a wani artabu da aka yi tsakanin jami'an tsaro da wasu 'yan bindiga a garin Darazo.

Wannan lamari dai ya faru ne yayin da 'yan bindigar suka kai hare-hare a lokaci guda a wani caji ofis na 'yan sanda da kuma wani banki wanda bashi da nisa daga caji ofis din.

Wannan lamari dai wata manuniya ce ga tabarbarewar tsaro inda ko a shekaranjiya wasu 'yan bindiga sun kasha wani dan sanda a garin Gombe mai makwabtaka da jihar Bauchin, kana wasu 'yanbindigar kuma suka kasha wani babban dan kasuwa mai suna Alhaji Adamu Na-kan-kwana a garin Wukari na Jihar Taraba mai makwabtaka da jihar Gombe.

Hakan kum ana faruwa ne baya ga tashe-tashen hankulla na kabilanci da na addini da ake fuskanta a jihar Filato da kuma matsalar 'yan Boko Haram a jihar Borno, duka kuma a daidai lokacin da zaben kasar baki daya ke kara kunno kai.