Boren Gabas ta Tsakiya ya tada farashin mai

Farashin mai
Image caption Wannan shi ne farashi mafi tsanani tun shekaru 2 da suka wuce

Tarzomar da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya ta sa farashin mai ya yi tashin gwauron zabi a kasuwannin duniya, inda yakai dola 104 kan ganga.

Farashin danyen mai samfarin North sea Brent, ya tashi zuwa Dala dari daya da hudu a kan kowace ganga, wanda shi ne farashi mafi tsanani tun shekaru biyu da suka wuce.

Wakilin BBC kan harkokin tattalin arziki ya ce lamarin zai iya kawo cikas ga hakar mai da ko kuma fitar da shi daga muhimman kasashe biyu masu samar da shi - Libya da Bahrain.

Ya kara da cewa lamuran siyasa a yankin Gabas ta Tsakiya nada dadadden tarihin sa farashin mai ya tsauwala.

A 'yan kwanakin da suka gabata, rikice-rikicen siyasa sun dabaibaye wasu daga cikin manyan kasashe masu arzikin man fetur, musamman ma Libya da Iran.

Babban abin da ya fi damun 'yan kasuwa dai shi ne yiwuwar samun tawaya a yawan man da kasashen ke samarwa ko fitarwa zuwa waje.

Hakan dai ya tura farashin danyen mai na Brent zuwa matakin da bai taba kaiwa ba a shekaru biyu da rabi.

Lokacin da rikicin ya yi kamari a Masar, farashin man fetur ya tashi ne saboda fargabar yiwuwar samun koma baya a safarar man ta mashigin Suez.

Sai dai kuma yayinda rikicin siyasa ke yaduwa zuwa manyan kasahen da ke fitar da man, kasuwannin duniya na fuskantar wata sabuwar barazana.