Jana'izar 'yan adawa a Bahrain

Bahrain Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wadanda suka halarci jana'izar sun yi Allah wadai da gwamnatin kasar

Dubun dubatar jama'a ne suka halarci sallar Juma'a a Bahrain kwana guda bayan da mutane uku suka mutu a tarzomar da ta barke tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga.

A wani masallaci, mabiya wani malamin Shi'a sun yi ife-ifen "nasara ga addinin musulunci" da kuma rushewar sarakunan kasar.

Tun da farko, sai da jama'a suka halarci jana'izar mutane ukun da aka kashe a ranar Alhamis. Wasunsu na cewa a shirye suke su mutu wajen kawo sauyi.

Ana saran masu goyon bayan gwamnati za su yi zanga-zanga sa'o'i kadan bayan da gwamnati ta haramta taron jama'a.

An jibge tankokin yaki a mihimman wurare na titunan birnin Manama, kwana guda bayan da aka tarwatsa masu zanga-zangar daga dandalin Pearl.

Ministan cikin gida na kasar ya ce jami'an tsaro za su yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da tsaro.

Gidan sarauta ne da mabiya tafarkin Sunni ke jagorantar kasar, amma akwai 'yan Shi'a da yawa a cikin masu zanga-zangar.

Babban malamin addnin Shi'a na kasar Sheikh Issa Qassem, ya bayyana harin da aka kaiwa masu zanga-zangar da cewa mummunan kisa ne, kuma gwamnati ta toshe kofar tattaunawa. A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Karin bayani