Baraka a jami'yyar PDP ta jihar Borno

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu yan siyasa a jahar Borno

A jihar Borno dake arewacin Najeriya rahotanni na nuna cewar Jam'iyyar PDP ta dakatar da tsohon dan takarar gwamnan jihar Alhaji Kashim Ibrahim Imam daga jam'iyyar.

Jami'yyar na zarginsa da cin amana, ta hanyar umartar dukkanin magoya bayansa dake jam'iyyar dasu sauya sheka zuwa Jam'iyyar ANPP mai mulkin jihar.

Jam'iyyar PDP ta bayyana cewar wannan shine mataki na farko data dauka, bayan da tsohon dan takarar yaki ya yi mata wani bayani, game da takardar da suka aike masa mai dauke da bayanan zargin da ake yi masa.

Alhaji Imam na daga cikin yan takara hudu da suka tsaya zaben fitar da gwani na jami'yyar a zabe me zuwa amma tun bayan da ya fadi a zaben ne jami'iyyar PDP ta fara zarginsa da hada kai da jamiyyar ANPP.