Zanga-zangar adawa da gwamnati a Djibouti

shugaba Ismael Omar Guelleh na Djibouti Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dangin Mr Guelleh ne ke ta mulkar kasar tun lokacin da ta samu 'yancin kai a 1977

Dubban jama'a ne suka fita kan tituna domin kira ga shugaban Djibouti Ismael Omar Guelleh ya yi murabus daga karagar mulki.

Ance jami'an tsaro na sa ido sosai kan masu zanga-zangar.

Dangin Mr Guelleh ne ke ta mulkar kasar tun lokacin da ta samu 'yancin kai daga Faransa a shekarar 1977. Amurka na da sansanin soji mai girma a kasar.

A bara ne aka gyara kundin tsarin mulkin kasar, domin baiwa Mr Guelleh damar tsaya wa zabe a karo na uku.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun ce za su zauna a filin wasan kwallon kafa na kasar har sai Mr Guelleh dan shekaru 63, ya bar mulki.

A watan Afrilu ne aka shirya gudanar da zabe. An sake zaben Mr Guelleh ba tare da hamayya ba a shekara ta 2005.

Masu zanga-zangar na dauke da kwalaye inda aka rubuta cewa "ba ma san IOG" kuma "ba mu yarda da zagaye na uku ba", kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.