Yau shekara guda da yin juyin mulki a jamhuriyar Nijer

A jamhuriyar Niger yau ne majalisar mulkin sojan kasar, ke cika shekara guda cif da hambarar da Mammadu Tandja daga mulki.

Bayan kifar da gwamnatin Malam MAMADOU TANDJA , majalisar Mulkin sojan ta yi alkawarin Farfado da tsarin mulki irin na dimukuradiyya tared a hadin kan 'yan kasa har ma da kokowa da Yunwa.

Ra'ayoyin 'yan kasar Niger dai sun banbanta a game da kamun hannun mulkin sojojin musamman ma a kan hada kan yan kasa.

Yayinda wasu ke zargin sojojin da yiwa wani bangaren yan kasar bita da kulli, wasu na cewa sojojin sun taka wata rawar a zo a gani.