Masu zanga zanga sun kwace iko da babban dandalin birnin Manama

masu zanga zanga a dandalin Pearl na Manama Hakkin mallakar hoto AP
Image caption masu zanga zanga a dandalin Pearl na Manama

Masu zanga-zanga a kasar Bahrain sun sake yin cincirindo a dandalin Pearl dake babban birnin kasar, wato Manama domin ci gaba da zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati.

Da farko dai 'yan sandan kwanatar da tarzoma sun durfafi masu zanga-zangar inda suka rinka harba barkonon tsohuwa da kananan bindigogi.

Amma daga baya kuma sai 'yan sandan suka sulale, suka bar gurin.

Masu zanga-zangar sun yi ta rera take suna neman gwamnatin kasar ta yi murabus, wadda sukai zargi da tauye hakki da kuma badakala.

Yarima mai jiran gado na kasar ta Bahrain Sheikh Salman bin Hamad Al-Khalifa, yana tattaunawa da shugabannin yan hamayyar, sannan ya ce yana iyakacin kokari domin ganin cewa al'amarin bai kara dagulewa ba.