Obama ya yi kira ga mahukuntan Bahrain

Yarima Salman Bin Khalifa Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yarima mai Jiran Gado Salman Bin Khalifa

Sojoji da 'yan sanda a kasar Bahrain sun kasance cikin shirin ko-ta-kwana tsawon daren jiya bayan zanga-zangar da aka gudanar bayan sallar Juma'a inda jami'an tsaro suka bude wuta a kan masu zanga-zanga.

'Yan adawa sun bayyana cewa an raunata masu zanga-zanga da dama lokacin da 'yan shi'a masu rinjaye a kasar ke jana'izar wasu matasa da aka kashe a farkon makon.

Gidan sarautar kasar ta Bahrain dai na fuskantar matsin lamba daga Amurka na ya guji amfani da karfi don murkushe zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Wannan sakon ne kuma gwamnatin Barack Obama ke son isarwa ga dukkan kasashen da ke fuskantar rikice-rikicen siyasa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Hukumomin kasar ta Bahrain dai sun dan nuna alamun rusunawa ga matsin lambar na Amurka ta hanyar tayin da Yarima mai Jiran Gado Salman Bin Khalifa ya yi na tattaunawa da al'ummar kasar, amma idan masu zanga-zangar suka koma gidajensu.

Sai dai masu zanga-zangar, wadanda 'yan Shi'a ne masu adawa da ci gaba da zama a karkashin mulkin 'yan Sunni, ba su amince da gwamnatin ba, don haka bukatarsu ita ce a sauya ta.

Su kuwa mahukuntan kasar, ga alamu suna jin cewa muhimmancinsu ga Amurka ya kai su yi watsi da matsin lambar na Amurka su kuma yi amfani da karfi a duk lokacin da suka so saboda kasancewar sansanin Runduna ta Biyar ta Sojojin Ruwa na Amurka a kasar.