Zargin dana bam a Enugu

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Rundunar 'yan sandan jahar Enugu a Najeriya ta ce, ta gano wani abu da ake zargin bam ne, a lokacin yakin neman zaben gwamnan jahar, Sullivan Chime, na jam'iyyar PDP.

Jami'an tsaron su ka ce suna cigaba da gudanar da bincike akan lamarin da ya faru jiya a Enugun.

Yayin da babban zaben watan Afrilu ke karatowa a Najeriyar, ana cigaba da samun tashe tashen hankula masu nasaba da siyasa.