'Ba za mu karya darajar Naira ba' -CBN

Sanusi Lamido Sanusi
Image caption Gwamnan Babban Bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi

Babban Bankin Najeriya, CBN, ya yi fatali da shawarar da Asusun ba da Lamuni na Duniya, IMF, ya ba shi a kan rage darajar Naira.

Bankin ya ce ya gamsu da darajar Nairar idan aka kwatanta ta da kudaden waje.

Kakakin Babban Bankin na Najeriya, Malam Muhammad Abdullahi, ya ce: “A ganinmu, yadda darajar Naira ta ke a yanzu ya dace da duk wasu alamu na tattalin arzikin kasarmu, da kuma kudaden shiga na waje da muke da su, musamman in aka yi la’akari da cewa wadannan kudaden—wadanda ake kira Foreign Reserve—za su iya taimaka mana wajen shigowa da kaya na watanni goma sha biyu, ba ma watanni uku da ka’ida ta bukata ba”.

A karshen makon nan ne dai Asusun na IMF ya nemi gwamnatin Najeriya ta rage darajar Nairar, to amma Babban Bankin na Najeriya ya ce Asusun bai ba da isassun hujjojin daukar wannan mataki ba.