An tura karin dakaru zuwa Benghazi na Libya

Masu zanga zangar kin jinin gwamnati a Libya
Image caption Masu zanga zangar kin jinin gwamnati a Libya

Rahotannin daga kasar Libya sun ce an tura wata rundunar sojoji ta musamman zuwa Benghazi domin kokarin sake karbar iko, bayan sababbin zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati da aka samu.

Wadanda suka gani da idanusu sun ce al'amarin ya kazanta bayan da sojojin suka durke jama'a da dama, yayinda masu zanga-zangar suka rinka mayar da martani ta yin jifa da duwatsu. A yau naji karar harbe-harbe, da fashe-fashe, sai dai ban sani ba ko daga masu zanga-zangar ne ko kuma daga dakarun Ghaddafi.

An rawaito cewa an ga motoci masu sulke suna cin wuta akan tituna.

Kasar Turkiyya ta ce al'amura suna kara tsamari a Libya, dan haka za ta tura jirgi domin kwaso 'yan kasarta.

Masu fafutukar kare hakkin bil'adama sun ce kimanin mutane tamanin da hudu sun rasa rayukansu sakamakon wadannan rikice-rikice a 'yan kwanakin da suka gabata.

Mahukuntan Libya dai sun gargadi masu zanga-zangar cewa za su gamu da gamonsu.