Asibitocin Benghazi sun cika makil

Zanga zanga a Benghazi
Image caption Zanga zanga a Benghazi

Likitoci a birnin Benghazi na Libiya sun ce ana cikin wani mummunan yanayi a can, kwana daya bayan da sojoji suka bude wuta akan masu halartar jana'izar wasu mutanen da dakarun tsaro suka kashe, a lokacin zanga zangar nuna kyamar gwamnati.

Wani likita ya ce, asibitoci sun cika makil da matattu, kuma kimanin mutane 900 suna kwance, sakamakon raunukan da suka samu.

Likitan ya ce, yawancin mutanen da suka mutun, an harbe su ne a kai, ko a wuya, ko kuma a kirji.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta kiyasta cewa, akalla mutane 170 ne suka hallaka, a tashe tashen hankulan da suka barke a Libiyar, a 'yan kwanakin nan.

A sauran biranen Libiyar kuma, rahotanni sun ce, ana artabu tsakanin masu zanga zanga da jami'an tsaro.

To sai dai babu cikakkun bayyanai, saboda an hana manema labarai fita daga Tripoli, babban birnin kasar.