'Masu zanga zanga sun kwace Benghazi'

Masu zanga zanga a Benghazi
Image caption Masu zanga zanga a Benghazi

Rahotanni daga kasar Libya sun ce masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati su ke iko da galibin birnin Benghazi, bayan wani gumurzu da jami'an tsaro.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce 'yan adawar sun kwace wani barikin soja mai matukar muhimmanci.

Wasu rahotannin kuma sun ce sojojin haya 'yan Afirka da gwamnatin Libiyar ta dauko, suna kai-kawo akan tituna.

Asibitoci sun rasa yadda za su yi da gawarwakin mutanen da aka kashe, ko kuma aka jikkata.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya William Hague, ya shaidawa dan shugaba Ghaddafi, Saif al Islam Gaddafi, cewa kasashen duniya zasu yi tir da matakan da gwamnatin ta dauka.

Libiya ta gargadi Tarayyar Turai akan cewa zata dakatar da hadin kan da take bata, wajen yaki da bakin haure daga arewacin Afirka, idan har ta ga cewa Kungiyar tana kara wa masu zanga zangar kwarin gwiwa.