Kura ta lafa a Dambatta

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Al'amura sun koma daidai a garin Dambatta a jahar Kano, bayan da aka samu wani tashin hankali tsakanin wasu mutanen garin da kuma 'yan sanda.

Tashin hankalin ya barke ne bayan da 'yan garin suka zargi 'yan sanda da dukan wani mutum da ake zargin ya saci babur duka, abinda yayi sanadiyyar mutuwarsa.

Mutanen garin sun yi zanga zanga domin nuna takaicinsu.

'Yan sanda sun yi harbi a sama domin tarwatsa su, abinda yayi sanadiyyar mutuwar wani almajiri.

Sai dai rundunar 'yan sandan jahar Kanon ta musanta cewa jami'anta ne suka daki mutumin da ake zargin barawo ne har suka zama ajalinsa.