Sojoji sun yi harbi a kan masu zanga-zanga

Wasu masu zanga-zanga a Benghazi
Image caption Wasu masu zanga-zanga a Benghazi

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun kasar Libya sun yi amfani da bindigogi masu sarrafa kansu da kuma manyan makamai don bude wuta a kan masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a birnin Benghazi.

Wadanda suka shaida faruwar al'amarin dai sun bayyana yanayin rudanin da aka shiga lokacin da sojoji suka rika harbi daga rufin gine-gine, yayinda masu zanga-zanga suka yi fito-na-fito da wadansu sojojin da ke kasa.

An dai bayar da rahoton kashe mutanen da ba a san yawansu ba, ciki har da kananan yara da kuma wadansu mutane akalla goma sha biyar wadanda ke wata jana'iza.

Wani mazaunin birnin ya shaidawa BBC abin da ya gani:

“Ina daura da kofar babban barikin soji; akwai kuma masu zanga-zanga ta lumana a waje, wadanda tun safe suke wurin sai kawai sojojin da suke ciki suka fara harbi da bindigogi masu sarrafa kansu, sannan kuma suka rika harba igwa a kan motoci.

“Mutane da yawa dai sun rasa rayukansu”.

Wani likita ya shaidawa BBC cewa an kai akalla gawarwaki takwas da kuma daruruwan wadanda suka yi rauni asibitin da ya ke aiki.

A cewarsa, akasarin wadanda suka rasa rayukansu an harbe su ne a ka, da kirji, da kuma ciki.

Karin bayani