NDLEA ta nemi a tsaurara yaki da kwayoyi

Jabun kwayoyi
Image caption Jabun kwayoyi a kasuwannin Najeriya

Hukumar da ke yaki da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya, wato NDLEA, na neman a tsaurara hukunci a kan masu ta'ammali da muggan kwayoyi a kasar.

Hukumar ta ce ya kamata a karfafa matakan yakar fataucin miyagun kwayoyin da ake da su a kasar, domin ta haka ne za a iya samun nasara.

Shugaban hukumar, Ahmadu Giyade, ya shaidawa BBC cewa “sha da safarar miyagun kwayoyi sun yi yawa; kuma ana kama mutane da yawa a Najeriya da kasashen waje, kuma suna batawa Najeriya suna matuka.

“Saboda haka nake ganin idan da so samu ne da fannin shari’a ya kara tsawatawa saboda dama doka ta ce duk wani wanda aka same shi da [laifin] safarar miyagun kwayoyi, a daure shi shekara biyar akalla.

“To amma sai ya zamanto yau idan mutum ya yi [wannan laifi] sai a daure shi ‘yan watanni kawai, wani ma a sake shi a beli; [kuma] a lokacin da ya ke belin sai ya [ci gaba] da safarar miyagun kwayoyin—ya je ya dawo ya je kotu”.

Sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya dai matsala ce da ke neman ta gagari kundila.

Ko a makon da ya gabata ma a Jihar Legas sai da aka kama wani mutum wanda ya hadiyi kimanin kullin kwayoyi dari da goma sha daya.