Yoweri Museveni ya lashe zaben Uganda

Yoweri Museveni Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yoweri Museveni

Yoweri Museveni ya lashe zaben shugaban kasar Uganda da kashi 67 cikin dari.

Abokin hamayyarsa, jagoran 'yan adawa, Dokta Kizza Besigye, ya sami kimanin kashi 26 cikin dari.

A cewar Dokta Besigyen, jam'iyya mai mulki ta yi amfani da makudan kudaden wajen sayen kuri'u.

Ya ce an tafka magudi a zaben, kuma ba zai amince da sakamakon ba.

Shugaba Yoweri Museveni ya kwashe shekaru 25 yana mulkin kasar ta Uganda.

In ji wakilin BBC, masu sa-ido na Tarayyar Turai sun ce, jam'iyya mai mulki ta yi amfani da ikon da take da shi, ta yadda sauran 'yan takara suka zama a takure.