Tawagar shugabannin Afrika zata Abidjan

Shugaban Afrika ta Kudu, Jacob Zuma, da wasu sauran shugabannin kasashen Afrika guda hudu, suna kan hanyarsu zuwa Kot Divuwa, don kokarin kawo karshen kiki-kakar siyasar da aka samu a can.

An kashe mutane akalla biyu a karshen mako, yayin da 'yansanda suka diram ma masu zanga-zangar goyon bayan Alassane Ouattara, mutumin da galibi ake dauka shi ne ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi a kasar a watan Nuwamba.

Shugaban da ke ci, Laurent Gbagbo, ya ki yarda ya sauka.

Jami'an tsaro na ci gaba da yin sintiri da tankokin yaki a wasu anguwannin birnin Abidjan.