'Mun harbe 'yan boko haram 5'- 'Yan sanda

Image caption 'Yan sandan Najeriya

Rahotanni daga jihar Borno a Najeriya sun ce da yau da safe rundunar 'yan snadan jihar ta bindige wasu mutane biyar da ake zargin 'yan Kungiyar nan ce ta Boko Haram a garin Damaturu na jihar Yobe.

Hakan ya biyo bayan wani samame ne da ta kai.

An kuma ce a sakamakon harin, 'yan sandan sun samu makamai masu dimbin yawa da suka hada da man yan bindigogi, da nakiyoyi, da albarusai sama da dubu biyu.

Hakan ya biyo bayan bayanan da rundunar ta ce ta samu a karshen makon nan lokacin da wasu dakarun soja suka cafke wasu mutanen da tarin makamai, a garin Gamborun Ngala yayin da suke shirin shiga da su Maiduguri daga kasar Kamaru.