Bayanai masu mahimmanci kan zaben Najeriya 2011

Zaben Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wannan zabe na da matukar mahimmanci ga Najeriya

Yakin neman zabe

1st Afirilu: Ranar karshe ta yakin neman zaben 'yan majalisar dokoki na kasa.

2nd Afirilu: Zaben 'yan majalisar dokoki.

8th Afirilu: Ranar karshe ta yakin neman zaben shugaban kasa.

9th Afirilu: Zaben shugaban kasa.

15th Afirilu: Ranar karshe ta yakin neman zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi. 16th Afirilu: Zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi.

Majalisar Dokoki

Majalisar dokokin Najeria tana da rassa biyu, Majalisar dattijai da ta wakilai:

Majalisar wakilai na da mambobi 360, yayin da ta dattawa ke da mambobi 109.

Majalisun biyu sun kunshi mambobi daga baki dayan jihohi 36 na kasar da kuma birnin tarayya Abuja.

Jam'iyyun Siyasa

Sama da jam'iyyu 60 ne ake dasu a Najeriya, amma manya a cikinsu su ne: Peoples Democratic Party PDP, Action Congress of Nigeria ACN, All Nigeria Peoples Party ANPP, Labour Party LP, All Progressive Grand Alliance APGA da kuma Congress for Progressive Change CPC.

Yawancin jam'iyyun na bin tsarin karba-karba ta yadda za'a rika juya shugabanci daga wannan yanki zuwa wani.

Wannan dai wani mataki ne na kaucewa ko rage korafe-korafen kaka gida na wani bangare.

Manyan Jam'iyyun Siyasa

Wasu jam'iyyu kalilan ne daga cikin jam'iyyu fiye da sittin da aka yi wa rajista suka mamaye siyasar Najeriya.

PDP

Tun bayan komawar kasar kan turbar demokradiyya a shekarar 1999, jam'iyyar PDP ke mulki a kasar.

Za'a iya kwatanta jam'iyyar a matsayin wadda ke dab da zama jam'iyyar kasa. PDP na da kujeru a duk fadin kasar, duk da cewa ta fi karfi a yankin tsakiyar Najeriya, gabashi da kuma kudancin kasar.

Jam'iyyar PDP ke shugabancin majalisun dokokin kasar, yayin da take da iko da kimanin kashi uku cikin hudu na majalisun jihohi da na gwamnonin kasar.

ACN

Jam'iyya ta biyu mafi girma ita ce Action Congress of Nigeria ACN, wadda tafi karfi ko rinjaye a Kudu maso Yammacin kasar, ko da yake bayan jihohin Legas, Ekiti da Osun jam'iyyar ce ke shugabancin jihar Edo wadda ke yankin Kudu maso Kudu.

Har ila yau jam'iyyar na da 'yayanta da aka zaba a majalisun dokokin kasar.

ANPP

All Nigeria Peoples Party ANPP ta fi karfi a Arewacin Najeriya, inda yawancin Hausawa ke mara mata baya.

Jam'iyyar ANPP dai ta yi ta samun koma baya tun shekara ta 2003, inda a yanzu take da gwamnoni uku.

CPC

Congress for Progressive Change CPC sabuwar jam'iyya ce wadda ta fi karfi a Arewacin Najeriya.

Tsohon shugaban kasar, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya ne ya kafa ta, da nufin cimma burinsa na shugabantar kasar, bayan abinda ya kira yankan bayan da tsohuwar jam'iyyarsa ta ANPP wadda yai takarar shugabancin kasar da bai nasara ba karkashinta yace ta yi masa.

Akwai kuma wasu jam'iyyu da suka hada da Labour Party LP (dake shugabancin jihar Ondo); All Progressive Grand Alliance APGA (dake da karfi a Kudu maso Gabashin kasar kuma take iko da jihar Anambra).

Duk da cewa akwai fiye da jam'iyyu 60 da aka yi wa rijista a Najeriya, sai dai kuma dukkansu in banda manyan jam'iyyun da aka Ambato a sama suna kawai suka tara.

A iya cewa jam'iyyun sun kasance wasu gungu-gungu ne dake kewaye da wasu 'yan siyasa masu karfin fada a ji a fannin siyasa.

Manyan 'Yan takara

Manyan 'yan siyasa hudu ne ke takarar kujerar shugaban kasa a zabukan da za'a yi a watan Afrilu:

  1. 1. Goodluck Ebele Jonathan - PDP- Shugaba mai ci. 2. Muhammadu Buhari - CPC - Tsohon shugaban kasa na soji. 3. Nuhu Ribadu - ACN- Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci a Najeriya EFCC. 4. Ibrahim Shekarau - ANPP - Gwamnan jihar Kano mai ci.

Babban kalubalen da jam'iyyar PDP mai mulkin kasar za ta fuskanta zai fito ne daga Muhammadu Buhari, wanda ke da karfi a yankunan karkara, musamman a Arewacin Najeriya.

Sai dai kuma gazawar da jam'iyyar CPC ta yi wajen yin hadaka da jam'iyar ACN wadda za ta bata karfi a Kudu maso Yammacin kasar ka iya ragewa jam'iyyar CPC din tasiri.

Karkashin tsarin hadakar da a da aka shirya, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ACN, Nuhu Ribadu zai janye ya barwa Buhari, inda ita kuma ACN din za ta zabi mataimakin shugaban kasa.

Me ake bukata domin samun nasara

Kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da kuma dokar zabe ta shekarar 2010 sun nuna cewa kafin a bayyana dan takarar shugaban kasar da ya yi nasara sai ya samu mafi yawan kuri'un da aka kada da kuma kashi 25% cikin dari na kashi biyu cikin uku na kuri'un da aka kada a duk jihohin kasar, ciki har da babban birnin tarayya (Abuja).

A watan Janairu na shekara ta 2011 ne majalisar dokokin kasar ta yi wa kundin tsarin mulkin kasar da ma dokar zabe gyaran fuska.