Gaddafi na fuskantar matsin lamba

Hakkin mallakar hoto gaddafi

Shugaban Libya, Kanar Gaddafi, yana fuskantar karin matsi a gida da waje, bayan da magoya bayansa suka maida martani da karfi a daren da ya gabata kan masu zanga-zangar kyamar gwamnati a Tripoli, babban birnin kasar.

Wani dan adawa ya sheda ma BBC cewa, hedikwatar jam'iyyar da ke mulkin kasar tana hannun 'yan hamayya.

Jagoran Kungiyar Kasashen Larabawa, Ams Moussa, ya bayyana bukatun masu zanga-zangar a matsayin na halas.

Akwai rahotanni dake bayyana cewa yanzu haka Kanal Gaddafi ya bar birnin Tripoli, ta yiwu zuwa garinsu dake Sirt ko kuma wani sansaninsa dake dajin Sabha.

Akwai labaran hare hare da aka kaiwa masu zanga zanga a cikin dare, musamman ma bayan rade radin cewa Kanal Gaddafi ya tsere daga kasar.

Hare-hare

Tashin hankalin ya sake zafafa ne bayan da dan Mu'ammamr Gaddafi wato Saif Al Islam Gaddafi ya bayyana ta akwatin gidan talabijin yana cewa mahaifinsa da dakarun tsaro zasu fafata iya karfinsu:

"Har yanzu sojoji na taka rawar a zo a gani, kuma suna da karfin yin haka."

"Yanzu haka dai sojojin za su sami ikon tabbatar da tsaro tare da tabbatar da cewa komai ya koma yanda yake ta kowacce hanya."

"Ba don komai ba, sai don hadin kan Libya da kuma makomar ta a gaba, don haka dole al'ummarta su tsaya da kafarsu."

"Sannan kuma zamu shaidawa mutane cewa sojin na da babban nauyi a wannan al'amari, don haka kuma ya kamata a sani cewa sojojin Libya ba kamar na Tunisia ko Masar bane."

Wani dan kasar wanda bai so, a ambace shi, ya ce;

"Sam ban yarda da maganganunsa ba. Ya dora alhakin akan kowa banda gwamnati, wannan bai dace ba."

"Ina ganin dai kawai yana so ne mutane su dinga fada da junansu. Wannan haka yake."

Bijirewa

Lokaci zuwa lokaci dai ana kara samun rahotannin barkewar tashin hankali.

Kusan dukkan shugabannin kabilu da shugabannin addinai dama manyan jakadun Libya sun bi bayan 'yan adawa.

Kusan za'a ce bangarorin dake gabashin kasar sun kubcewa ikon gwanati.

Wanda hakan ke nuni da cewa karfin ikon kanal Gaddafin sannu a hankali na kara rauni.

Abubuwan dake faruwa a kan titunan Tripoli dai sune za su tabbatar da makomar mulkin kimanin shekaru arba'in da Kanal Gaddafi ya shafe yana yi a Libya.