Mutane 2,000 sun yi zanga-zanga a Morocco

Masu zanga-zanga a Morocco Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga-zanga a Morocco

Fiye da mutane dubu biyu ne su ka gudanar da zanga-zanga a Rabat, babban birnin Morocco, suna neman Sarki Muhammad na Shida ya rage karfin ikonsa ya kuma yaki rashawa da talauci.

Masu zanga-zangar, wadanda yawancinsu matasa ne, sun ce suna bukatar sabuwar gwamnati amma suna goyon bayan sarkinsu.

Wata daga cikin masu zanga-zangar ta ce: “Muna bukatar kundin tsarin mulki ya amince da harshenmu tare da Larabci.

“Muna kuma bukatar al'umma ta samu cikakken 'yancin samun ilimi, da lafiya, watau dai ilimi ga kowa”.

'Yan sanda sun shiga cikin masu zanga-zangar amma ba su hana ba.

An kuma gudanar da gangami a garuruwan Casablanca da Marrakesh.

Karin bayani