Fargaba dangane da zabubbukan Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

A Najeriya, yayin da zabubbukan kasar ke dada karatowa, ana ta bayyana fargaba cewa, mai yiwuwa rikice-rikice su kawo cikas ga gudanar zaben.

Hakan na zuwa yayinda ake ta samun rahotannin shigar da makamai kasar, da tashe-tashen bama-bamai da kisan gillar da ake yi wa mashahuran 'yan siyasa.

Ko a karshen makon da ya gabata, rundunar ’yansandan kasar a Jihar Enugu da ke kudu maso gabashin kasar ta yi ikirarin cewa ta gano wani abu wanda ake zargin bom ne a harabar dandalin da gwamnan Jihar ya kaddamar da gangamin yakin neman zabensa.

Da ma dai a can baya, wadansu bama-bamai sun tashi lokacin da ake bikin cika shekaru hamsin da samun ‘yancin Najeriya a watan Oktoban bara.

Hukumar kwastam ta kasa kuma ta ce ta lura an samu karuwar shigo da motoci wadanda harsashi ba ya iya hudawa.

Ana ma zargin Najeriya ta zama matattara makamai.

Wadannan al’amura sun haddasa fargaba da tababa dangane da yiwuwar gudanar da zabe mai inganci cikin kwanciyar hankali.