Dubban mutane za su mutu sanadiyyar shan giya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Barasa

Rashin ingantacciyar dokar shan giya za ta yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu dari biyu da hamsin a Ingila da Wales nan da shekaru 20, In ji likitoci.

A wani rubutu da ya yi a Kasidar 'The Lancet', wani masani kan cutar hanta ya ce dole ne a tsaurara matakan rage yadda ake shan giya wanda kuma ya hada da kara kudin ta.

Likitoci sun bayyana kusancin gwamnatin hadin gwiwar Burtaniya da kamfanonin barasa a matsayin hatsari ga aiwatar da dokar.

Amma Hukumar kula da Lafiya a Burtaniya ta ce tana daukar kwararen matakai domin rage shan barasa, a yayin da suma kamfanonin barasar ke cewa suna yin duk mai yiwu domin hana shan barasa ba bisa ka'ida ba.

Masana ilimin kimiya a Burtaniya sunyi hasashen cewa mutane da dama ne za su mutu sanadiyar ciwon hanta.

Masanan na ganin dole ne Burtaniya ta yi koyi da yadda Faransa ta mangance matsalar shan giya a shekarun 1960, inda akai ta fama da ciwon hanta sanadiyyar shan giya.

Faransa ta tsaurara matakan shan giya ne a wannan lokacin kafin ta samu saukin al'amarin.

Tsaurara doka

Likitoci sun ce muddin aka tsaurara dokar shan giya a Burtaniya za'a samu raguwar mutanen dake mutuwa sanadiyyar shan giya da kashi uku.

Amma sun yi gargadin cewa za'a samu karuwar masu mutuwa sanadiyyar shan giya ta hanyar ciwon daji da kuma hadarurruka, a inda su ke cewa sama da mutane dubu dari biyu da hamsin ne za su mutu sanadiyar shan giya a Ingila da Wales nan da shekaru 20 masu zuwa.

Kungiyar likitocin da Farfesa Sir Ian Gilmore ya jagoranta na gangamin neman tsauraro dokokin shan giya a Burtaniya, a yayinda su kai yi murhabin da karin harajin da gwamnatin Burtaniya ta yi na kashi biyu kan kamfanonin sarrafa barasa a kasar.

Amma sun ce dokar da ake amfani da ita a yanzu haka ba za ta yi tasiri ba, ganin cewa ba za ta hana mutane shan giyar ba.

"dole ne a kara kudin barasa, saboda kada a bar kowa ya iya siya musamman idan aka yi la'akari da hatsarin da ke tattare da ita." In ji Sir Ian.

"Barasa kamar kwaya ce, Kuma a halartata a Burtaniya, amma kwaya ce da kusan mutane miliyan daya da rabi ke sha, ya kamata a tsaurara dokokin kan shan ta kamar yadda aka yi a kan taba."

Ya kara da cewa 'yan majalisa sun zargi ministocin gwamnati da kin sauraren masana a harkar lafiya saboda kusancinsu da kamfanonin sarrafa barasa.

Sir Richard Thompson, Shugaban Likitoci na Royal College of Physicians, ya ce: "dole ne gwamnati ta dau wannan batun da mahimmacin saboda irin mutuwar da ake yi. Yadda ake maida hankali kan rage shan taba, dole ne a yi wani abu kan hana shan giya."

Mai magana da yawun kamfanin siyar da barasa ya ce;" Likitocin ba su la'akari da ganin yadda mu ke biyan haraji mai dubbin yawa ba."

"A fadin Turai, a Burtaniya duk an fi biyan haraji kan barasa, a Faransa ba a tsauwala musu haraji ba, amma sun rage yawan wadanda ke mutuwa sanadiyyar ciwon hanta."

Ya kara da cewa kamfanonin barasa sun sha alwashin rage yadda ake shan giya ba bisa kan ka'aida ba.