Kwamitin Sulhu ya sa wa Libya takunkumi

Hakkin mallakar hoto AFP

Bayan shafe tsawon lokaci ana tafka zazzafar muhawara game da ko shin ya cancanta a gurfanar da Libya a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa, ICC, domin ta binciki zargin aikata laifukan yaki ko a'a, musamman ma tare da tunanin ko shin Sin za ta amince da haka, a karshe dai sai jakadanta ya daga hannun sama kamar yadda saura suka yi.

Ya kara da bayyana yadda Beijing ke bayar da goyon bayanta akan magance abubuwan da ke faruwa a Libya.

Duk da dai cewa wasu daga cikin jakadun sun yi shakkar kada su janyo abinda zai zo ya dame su daga baya, kungiyar tarayyar turai cewa ta yi ya kamata a tabbatar da haka domin ta haka ne kawai za'a aike da sakon gargadi ga Kanar Gaddafi da jami'ansa.

Kudurin kwamitin ya saka wasu karin takunkumi akan shugabannin Libya.

Wannan ya hada da haramcin tafiye tafiye da kuma hana Kanar Gaddafi da iyalansa da kuma manyan jami'ansa taba dukiyoyinsu dake waje.

Lamarin da dama tuni Amurka ma ta zartar da irinsa kan dukiyar dake ajiye a kasar ta.

Tuni kuma ita ma kungiyar tarayyar turai ta dauki mataki makamancin wannan.

Duk da dai cewa kudurin kwamitin bai bayar da umarnin baiwa al'umma kariya daga harin da dakarun Libyan ke kai musu ba, ya dai bayyana cewa ya kamata mambobin kasashe du dauki duk matakin da suka ga ya kamata wajen agazawa ba wai babatu kawai ba.