Girgizar kasa: Mutane 65 sun rasu a New Zealand

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Pira Ministan New Zealand ya ce akalla mutane 65 ne su ka mutu a girgizar kasa a birnin Christchurch.

John Key ya ce ana kyautata zaton za'a samu karin wadanda su ka mutu, a yayinda wasu da dama ke jinya.

Girgizar kasar ta faru ne a dai dai lokacin da jama'a su ka cika makil a brinin na Christchurch da rana.

Magajin garin Christchurch ya ce an ceto wajen mutane 120 a girgizar kasar.

Har yanzu dai ana ci gaba da aikin ceton wadanda su ke raye a baraguzan gine-ginen da su ka rushe.