An kashe mutane akalla goma a kauyen Fan

Rahotanni daga jihar Filaton Nijeriya na cewa mutane sama da goma sun rasa rayukansu a wani farmaki da wasu mutane da ba a tabbatar ko su wane ne ba suka kai a jiya da dare a wani kauye dake gundumar Fan a yankin Barikin Ladi.

Yayinda wasu mazauna kauyen ke zargin wasu Fulani da kai harin, wani jagoran Fulani makiyaya da aka tuntuba ya musanta zargin.

Rundunar tsaro dake aiki a jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin kuma ta ce tana kan gudanar da bincike.

Jihar ta Filato dai ta dade tana fuskantar tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini, da kuma siyasa inda dubban mutane suka rasa rayukansu a cikin 'yan shekarun nan.