Kasashen duniya na taro kan kasar Libya

Mu'ammar Gaddafi na Libya Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)
Image caption Mu'ammar Gaddafi na Libya

Jami'an diflomasiyya na ta kokarin samar da mafita game da rikicin kasar Libya dake dada ruruwa, bayan kusan mako guda ana zanga zangar kin jinin gwamnati da kuma kazamin ba-ta-kashi a kasar.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na gab da gudanar da wani taro cikin sirri a yau, kuma kungiyar hadin kan Larabawa za ta tattauna a yau a birnin Alkahira.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana damuwarsa game da almarin na kasar ta Libya.

An ga Shugaba Gaddafi a wata hira a talabijin, wadda ba ta kai tsawon minti daya ba, yana musanta cewa ya gudu ya bar kasar.