Gaddafi yayi jawabin bijirewa

Mu'ammar Gaddafi na Libya Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)
Image caption Mu'ammar Gaddafi na Libya

Shugaban kasar Libya Kanar Muammar Gaddafi yayi kira ga magoyabayansa da su fita kan tituna su murkushe wadanda ya kira kyankyasan da suke zanga zangar adawa da shi.

Ya yi kira ga masu biyayya ga kasar Libya da su yi farautar masu adawa da gwmanati dake zanga zanga, su kamo su, sannan su mika su ga hukumomin tsaro.

Ya ce "kuna so ne Amurka ta zo ta mamaye kasarku kamar Afghanistan da Somalia, da Pakistan da Iraq. Abinda kuke so kenan.Abinda zai faru kenan ga kasarmu, mu koma kamar Afghanistan. Abinda kuke so kenan.

Idan haka kuke so to, idan kuwa ba kwa son haka, to ku hau kan tituna ku kamo su, ku kwace makamansu".

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar hadin kan Larabawa na gudanar da wani taron gaggawa domin tattaunawa kan rikicin kasar Libya.

Majalisar Dinkin Duniya za ta fara muhara nan ba da jimawa ba.

Mataimakin jakadan Libya a

Majalisar Dinkin Duniya Ibrahim Al Dabbash ya bayyana irin abinda yake son a cimma a taron na Majalisar Dinkin Duniya.

Ya ce "kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zata gana a yau.Za mu yi kokarin fitar da sanarwar kaddamar da dokar hana sauka da tashin jiragen sama a Libya, domin hana kai hare hare akan biranen Libya, domin dakatar da sojojinda gwamnati za ta dauko haya daga ketare, kuma domin hana makamai kaiwa ga gwamnatin kama karya".